Likitoci sun yi jan hankali ga mutanen da suke fama da cututuka kamar ciown suga da hawan jinni da kuma kyambon ciki a kan abincin da zasu rika bude baki da shi domin kawo rigakafi ga cututukan da suke fama da su.
Dokto Manu Ahamdu kwararren likita a Jamhuriyar Nijar ya bayyana cewa, idan mutum yana da kiba sosai yana da bukatar ya rage cin abinci mai kitse. Yace mai ciwon suga yana kuma bukata ya rafe shan wani abu ko ruwa mai yawan suga domin zai iya kawo mashi matsala yasa ciwon sugan ya tsananta.
Haka kuma cin abinci mai barkono da yawa yana da hatsari ga wanda yake fama da ciwon gyambon ciki ko shan abu mai tsami ba tare da sun ci wani abinci ba tukuna.
Likitan yace zai zama da amfani idan masu fama da wadannan cututuka suna kula da kiyaye abinda zasu ci.