Gargadin zai ce "shan lemu da aka karawa sukari yana iya haddasa kiba, da cutar sukari watau diabetes, da kuma rubewar hakori." Tilas a duk tallace-tallacen lemun da wasu kayan shaye shaye na zamani da aka karawa sikari, da ake tallarsu akan irin manyan allunan tallan nan, ko a jikin motoci kiya-kiya, ko a tashoshin shiga mota, ko akan manyan takardu, ko a dandalin wasanni a birnin na San Francisco.
Sai dai ba za'a bukaci wannan gargadin ba, a tallace tallacen da kamfanonin zasu yi a gidajen talabijin ko rediyo.
Illahirin kansiloli a majalisar karamar hukumar birnin ne suka amince da wannan doka wacce zata fara aiki ranar 25 ga watan Yuli. Haka nan dokar ta haramtawa rassa da hukumomi gwamnatin karamar hukumar daga amfani da kudaden daga baitul malin gwamnati wajen saye lemunan da aka karawa sukari.