Rahotanni sun ce komai na gudana kamar yadda aka tsara a Addis Ababa, babban birnin kasar, inda aka samu dogayen layukan masu kada kuri’a.
Jam’iyyun adawa sun yi ikrarin cewa zaben ba shi da sahihanci domin hukumomin kasar suna kama ‘yan adawa da masu shafukan internet da kuma ‘yan jarida.
Koda yake jam’iyyar ta EPRDF ta musanta wadannan zargin.
A zaben shekarar 2010, jam’iyyar ta lashe kusan dukkanin kujerun ‘yan majalisu, wanda zabe ne da aka gudanar cikin lumana, ba kamar wanda aka yi a shekarar 2005 ba, wanda ya haifar da mummunan rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 200.
Akalla mutane miliyan 37 ne ake sa ran za su kada kuri’unsu a wannan zabe, ana kuma sa ran samun sakamakon zabe nan da tsakanin kwanaki biyu zuwa biyar.
Wakilan kungiyar tarayyar Afrika su 59, sun kasance sune kadai masu sa-ido a wannan zabe, domin ba a gayyaci cibiyar nan ta Carter Centre da ke Amurka da kuma kungiyar tarayya turai ba, kamar yadda aka yi a zabukan da suka gabata.
Wadannan zabuka, sun kasance sune na farko, tun bayan mutuwar tsohon Firai ministan kasar Meles Zenawi a shekarar 2012.
Ana sa ran Firai minister mai ci a yanzu, Haliemariam Desalegn zai ci gaba da kasancewa akan karagar mulki bayan zaben.