Shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban kasar Ghana John Dramani ya gargadi takwarorinsa da suka halarci taron kolin na 47 a Accra babban birnin Ghana da su mayarda hankali wurin samarwa matasansu ayyukan yi.
Shugaba John Dramani yace karuwan matasa da basu da aikin yi na yiwa zaman lafiyar kasashen barazana da kuma dakile cigaban kasashen. Yace karuwan matasa nada albarka amma rashin samar masu da aiki na tafe da hadarin gaske. Yace ya kamata su mayarda hankali akan rayuwar matasa. Yace yana kyautata zaton ECOWAS zata sa maganar matasa gaba a taronta na gaba.
Dr Bab Watche masanin tattalin arziki ya yi nazari akan rashin aikin yi ga matasa. Yace dalilai da dama suka yi sanadiyar rashin aikin yin ciki har da rashin fadada ayyuka a kasashen ECOWAS din. Saidai ya kara da cewa matsalar ba ta yammacin Afirka ba ce kadai. Kasashen duniya da dama suna fama da ita kamar kasar Afirka Ta Kudu inda kashi hamsin cikin dari na matasan kasar basu da aikin yi lamarin da ya yi sanadiyar hare-hare a kan baki dake zaune cikin kasar. Kazalika Tunisia ma tana fama da matsalar wadda ta janyo mata bori. Idan shugabannin yammacin Afirka na neman su zauna lafiya to sai sun mayar da hankali akan samar ma matasa aiki.
Daga karshe mahalarta taron sun yabawa Najeriya da yin zabe cikin lumana. Sun jinjinawa shugaban kasar mai barin gado Goodluck Jonathan da yin zabe da amincewa da sakamakon zaben cikin kwanciyar hankali. Shugaban Ghana ya karanta yabo na musamman wa Shugaba Jonathan. Shugaban ya yi fatan za'a gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a wasu kasashen kamar yadda aka yi a Najeriya.
Ga rahoton Yakubu Baba Makeri.