Wannan alwashi na zuwa makwanni kadan bayan da kungiyar ‘yan tawayen FPL ta dauki alhakin fasa bututun kusa da rijiyoyin mai na Agadem yayin da kuma hukumomin mulkin soja na CNSP suka fara duba yiwuwar fitar da danyen mai ta tashar jirgin Ruwan Kribi a kasar Kamaru ratsawa ta Chadi.
A karshen ganawarsu da shugaban majalissar CNSP Janar Abdourahamane Tiani a birnin Yamai, fadar gwamnatin Nijar, shugabanin al’ummar kabilar Tubawa da suka hada da na yankin Kawar da N’gourti da Tesker sun bayyana cewa sun zo ne domin jaddada wa hukumomi hadin kai a yunkurin tabbatar da tsaro.
Kuma suka ce saboda haka a shirye suke su bada duk gudunmawar da ta dace domin tunkarar sabon al’amarin da ya bullo a yankin mai arzikin man fetur inda a tsakiyar watan Yunin da ya gabata wata kungiya, FLP, ta dauki alhakin fasa bututun mai a yankin Zinder.
Jagoran wannan tawwaga ta shugabanin al’ummar kabilar Tubawa Alhaji Adam Ousseini ya bayyana cewa za su nemi hadin kan jama’a don ganin irin haka ba ta sake faruwa ba.
Masu fashin baki a kan sha’anin tsaro a yankin gabashin na Nijar irin su Mara Mamadou na kungiyar AEC na ganin fa’idar wannan ganawa ta hukumomi da shugabanin al’umma domin a cewarsa ingantacciyar hanya ce da za ta bada damar murkushe tarzomar da aka fara fuskanta.
Shi ma wani dan fafutika Moustapha Ali Adam da ya yaba da wannan mataki na tuntuba ya shawarci mahukunta su fadada abin zuwa sauran yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.
Wannan yunkuri na samar da tsaro a yankunan da Nijar ke hako man fetur da ma wuraren da bututun ya ratsa na zuwa a wani lokacin da hukumomin kasar suka bayyana shirin daukan matakan fara fitar da man ta kasashen Chadi da Kamaru zuwa tashar jirgin Ruwan Kribi.
Maganar da a yau ake tattaunawa tsakanin jami’an kamfanin dillancin mai na kasa SONIDEP da wata tawwagar jami’an Chadi da suka zo Yamai takanas ke nan. Yayin da ayyukan bututun Nijar-Benin suka tsaya cik sanadiyar takun sakar da ta taso a tsakanin mahukuntan kasashen biyu.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5