An Gudanar Da Taron Musayar Ra'ayi Domin Hana Matasa Zama Masu Ra'ayin Rikau

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka da hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu zaman kansu, sun gudanar da musayar ra’ayi akan yadda za’a hana matasa zama masu ra’ayin rikau.

Tarom mai taken zama kan ra’ayin rikau, rawar da matasa da matasa da gwamnati ta kamata su taka, ma’aikatar ta ce ta gayyato matasa ne dake da kungiyoyin ayyukan sa kai musamman domin matasan, yawancin matasan da suka halarci taron sun fito ne daga wuraren da ke fama da rikici mai nasaba da matasa, kuma kowannen su yayi bayanin irin ayyukan da kungiyarsa ke yi.

Daya bayan daya Matasan sun bayyana irin matsalolin da suka addabi matasan kasashen su, da kuma bada shawarwari akan hanyoyin da suke ganin zasu fi dacewa a bi domin shawo kan matsalolin.

Haka kuma taron ya bayyana dalilan dake sa yawancin matasan zama masu ra’ayin rikau, da dama daga cikin matasan da suka tsunduma kawunansu cikin irin wannan yanayi a sakamakon rashin damawa da su a harkokin da suka shafe su, da kuma rashin bayani da gwamnati bata yi akan wasu harkokin tafiyar da kasa da suka kamata jama’a su sani.

Ma’aikatar ta bayyana cewa ta shirya wannan ganawar ce domin lalubo hanyar da matasa ke jin ta dace a bi domin shawo kan irin wadannan matsaloli na ra’ayin rikau wanda shike haifar da ta’addanci.

Fatima Shu’aibu Askira, matashiya ce wadda ta sami gayyatar wannan taro daga Najeriya domin itama ta bada irin tata gudummuwar domin a shawo kan matasa daga wannan mummunar dabi’a, inda ta sami zantawa da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Ladan Ibrahim Ayawa.

Ga cikakken rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanar Da Taron Musayar Ra'ayi Domin Hana Matasa Zama Masu Ra'ayin Rikau