Kungiyar NSRP mai rajin wanzar da zaman lafiya a Najeriya, dake karkashin kulawar hukumar raya kasashe ta kasar Birtaniya DFID, itace ta shirya taron ga manyan ‘yan jarida a Kano, musammanma shugabannin kafofin labarai.
Mallam Aminu Buba Dibal, shine babban jami’in kungiyar a shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya, yace “mun shirya taron ne domin inganta yadda gidajen radiyo da duk kafafen yada labarai zasu inganta yadda suke aiki, musammanma alaka da ake iya samu ta rashin iya aiki da zai kawo tashin hankali a wajen al’umma.”
Daya daga cikin manyan jami’an bada shawarwari kan aikace aikacen hulda da kafofin labarai a hukumar ta DFID, Alhaji Umar Sa’idu Tudun Wada, ya gabatar da makala kan dabarun bada rahotanni a yayin tarzoma da yake yake.
Shima Prince Daniel Aboki, da ke zaman shugaban tashohin Wazobia FM da Arewa Fm da kuma Cool FM, ya fayyace nauyin da ya rataya a wuyan shugabannin kafofin labarai, inda yace yakamata ace duk shirye shiryen da za a yi ana yinsa ne bisa tsari ya zamanto da tsafta.
Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.
Your browser doesn’t support HTML5