NIAMEY, NIGER - Sun ware ranar musamman nr domin gudanar da bukin farfado da al’adunsu yayinda a dai gefe wannan buki ke hangen karfafa dangantaka a tsakaninsu da sauran al’umomin da suke zaune tare.
Wannan shi ne karo na biyu da al’ummar Tubawa ta Nijar ke shirya irin wannan bukin na raya al’adunsu da ke matsayin daya daga cikin kabilu 10 da aka tabbatar da su a hukunce a wannan kasa.
Gwadawa abokan zama al’adun kabilar ta Tubawa na daga cikin dalilan kirkiro da wannan buki kamar yadda Lamine Kidde mamba a kwamitin tsare-tsare ya bayyana mana.
Tubawa wadanda suka rungumi kiwo da kasuwanci a matsayin abin dogaro mutane ne dake zaune a karkara to amma yawaitar wadanda ke kaura zuwa birane a ‘yan shekarun nan wani abu ne da aka gano cewa ya na barazanar batar da al’adun kabilar ta Tubawa, saboda haka wannan buki ke hangen cusa kishin hakan a zuciyar yaran Tubawa.
Kasancewar al’adu na matsayin wata hanyar karfafa dankon zumunta da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomi masu al’adu mabambanta ya sa aka karkatar da bukin na bana akan batun raya al’adu.
Alkaluman kididigar 2020 sun yi nuni da cewa Tubawa sama da million biyar ne ke zaune a tsakiyar yankin arewacin hamadar Sahara wato arewacin Chadi da kudancin Libya da kuma arewa maso gabascin Nijar inda suke zaune shekaru aru-aru da sauran kabilun jihohin Damagaram Diffa da Agadez.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5