An Gudanar Da Bikin Yaye Sabbin Hafsoshin Da Suka Karanta Dubarun Yaki A Nijar

An Gudanar Da Bikin Yaye Sabbin Hafsoshin Da Suka Karanta Dabarun Yaki A Nijar

A jamhuriyar Nijar yau aka yi bukin yaye wasu sabbin hafsoshin da suka shafe watanni 8 suna karantar dubarun yaki a matsayin wani bangare na yunkurin da hukumomin kasar suka sa gaba wajen neman hanyoyin tunkarar kalubalen tsaron da ake fama da su a ‘yan shekarun nan.

NIAMEY, NIGER - Gomman barade daga rundunonin daban-daban na kasar ta Nijar ne suka kammala karatu a makarantar horon hafsoshi ta birnin Yamai wato Ecole Militaire Superieure wacce shugaban kasa Mohamed Bazoum ya kaddamar da soma ayyukanta a watan Oktoban 2021 da nufin soma horar da manyan hafsoshin soja dubarun yaki a nan cikin gida.

Hakan dai na faruwa ne sabanin yadda a can baya ake tura irin wadanan askarawa kasashen waje don daukar horo duk kuwa da cewa yanayin tsaron kasashe sun sha bam-ban daga wannan zuwa waccan.

An Gudanar Da Bikin Yaye Sabbin Hafsoshin Da Suka Karanta Dabarun Yaki A Nijar

Rukunin farko na daliban babbar makarantar horon soja na kunshe da askarawa 26 da suka fito daga rundunoni daban daban wadanda suka hada da hafsohi 2 na rundunar tsaron jandarma da hafsoshi 2 na rundunar Garde Nationale sai hafsoshin soja 22 daga rundunar mayakan kasa.

An Gudanar Da Bikin Yaye Sabbin Hafsoshin Da Suka Karanta Dabarun Yaki A Nijar

A tsawon wadannan watanni hafsoshi sun dauki darussa akan dubarun yaki daga abinda ya shafi jagorancin rundunar cikin gida a fagen daga har ma da na rundunar kasa da kasa.

Ministan tsaron kasa Alkassoum Indatou wanne ya jagoranci wannan buki ya yi tunatarwa akan harin da ‘yan ta’adda suka kaiwa jam’ian tsaro a jiya talata inda jandarmomi 8 suka rasu 33 suka ji rauni. Saboda haka ya gargadi wadanan sabbin hafsoshi a game da aikin dake jiransu a fagen daga.

An Gudanar Da Bikin Yaye Sabbin Hafsoshin Da Suka Karanta Dabarun Yaki A Nijar

Ya ce za su yi aiki ne a cikin wani yanayin tsaro mai sarkakiya, wannan zai basu damar bada gudunmowar da ta dace a ayyukan tabbatar da tsaron kasa da al’umma baki daya. Idan aka dubi halin da ake ciki a yau kasar na matsayin wata ganuwar dake hana wa ta’addanci yaduwa a wannan yanki.

An Gudanar Da Bikin Yaye Sabbin Hafsoshin Da Suka Karanta Dabarun Yaki A Nijar

An Gudanar Da Bikin Yaye Sabbin Hafsoshin Da Suka Karanta Dabarun Yaki A Nijar

Juriya da jimirin sojojin kasar abu ne dake kara kima a idon abokan tafiya saboda yadda aka hana ‘yan ta’adda kafa sansani a kasar kuma akan ba makwafta dauki idan bukata ta taso a cewarsa.

Jamhuriyar Nijar dake tsakiyar yankin Sahel na kewaye da kasashen masu fama da tashe tashen hankula dalili kenan hukumomi suka dage wajen karfafa matakai ta kowane bangare.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanar Da Bikin Yaye Sabbin Hafsoshi Da Suka Karanta Dubarun Yaki A Nijar