Yau 1 ga watan Mayu, rana ce da aka tsayar a matsayin ranar ma’aikata ta duniya inda kasashe daban daban ke yin bukin wannan rana ta hanyoyi daban daban.
Sai dai a Jamhuriyar Nijar, ranar ta kasance ranar addu’o’i ce musamman domin tunawa da dakarun kasar da suka rasa rayukansu a fagen daga a sanadiyyar harin da ‘yan Boko haram suka kai ranar 25 ga watan Afirilun da ya gabata a wani sansanin sojojin da ke tsibirin Karamga a tafkin Chadi.
A jahar Mardin Jamhuriyar Nijar, kungiyoyin ma’aikata 11 suka hada kansu domin gudanar da addu’o’i, a cikin wadanda suka jagoranci addu’o’in sun hada da limamin masallacin juma’a Malam Adamu Musa ‘Yan Tuma da kuma shugaban hadakar kungiyoyi jahar Maradi Malam Sahabi Ibrahim, wanda yayi godiya da rokon Allah yasa addu’ar ta kai ga mamatan da kuma iyalansu.
Masu jagorancin, wato Malam Yahaya Godi, babban sakatare a fadar gwamnan jahar Maradi ya yi karin bayanin cewar sanin ya kamata ne yasa suka dukufa domin yin wadannan addu’o’i musamman bisa la’akari da dalilan da suka yi sanadiyyar rayukan sojojin wanda sadaukar da kai ne domin bada kariya ga kasa.
Daga karshe an gudanar da sauran addu’o’i domin neman zaman lafiyar kasa da ci gabanta. An yi wadannan addu’a’i ne a babban masallacin juma’ar Alhaji Zungiri da ke hanyar Dan Isa a jahar Maradi.
Your browser doesn’t support HTML5