Rahotanni daga Peru na cewa an garzaya da tsohon shugaban kasar Alberto Fujimori zuwa asibiti.
An kai Fujimori asibiti ne daga gidan yari, inda yake zaman hukuncin shekaru 25 da aka yanke masa.
Dan shekaru 79, Fujimori, na zaman gidan yari ne bayan an same shi da laifin cin zarafin bil adama da kuma gudanar da wani gungun mutane da suka kware wajen kisa a lokacin da ya yi mulki a tsakanin shekarun 1990 - 2000.
“Ya dan galabaita, abin yana da dan rikitarwa,” Inji likitan Fujimori, Alejandro Aguinaga.
Rahotanni sun ce tsohon shugaban yana fama ne da matsalar gudanar jini a sassan jikinsa da kuma matsalar bugun zuciya.
Bayanai sun yi nuni da cewa ya taba samun irin wannan matsala a baya.
Idan har ya kammala wa’adinsa na zaman gidan yari, Fujimori wanda aka rufe shi tun a shekarar 2005 zai fito yana mai shekaru 93.
Sau uku yana neman afuwa, amma duk aka ki amincewa saboda likitoci sun ce ba ya tattare da wata cuta da ke nuna zai mutu nan da wani lokaci.
A karkashin dokar kasar Peru, har sai mutum yana da wata cuta da ta nuna zai mutu nan da wani lokaci kafin shugaban kasa ya yi mai afuwa.
Sannan ba shi da wata matsalar ta tabin hankali, wanda shi ma dalili ne da zai sa a yi afuwa.
A baya shugaban Peru, Pedro Kuczynski, ya ce zai yanke shawara nan da karshen shekarar nan kan ko zai yi wa Fujimori afuwa bisa dalilai na rashin lafiya.