Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Kasan Amtrak Ya Fadi a Amurka


Jirgin da ya kauce layi, wasu taragunsa sun rikito kan hanya
Jirgin da ya kauce layi, wasu taragunsa sun rikito kan hanya

Yau da safe jirgin kasa mai mai dan karan gudu da ya taso daga birnin Seatle cikin jihar Washington kan hanyarsa ta zuwa birnin Portlad a jihar Oregon, ya kauce layinsa wasu taragunsa suka rikito kasa.

Wani jirgin kasan kamfanin Amtrak ya kauce hanyar da ke kan wata gada, ya rikito a kan titi a jihar Washington da ke Arewa maso kudancin Amurka.

Rahotanni sun ce mutane da yawa sun ji rauni amman jami’ai ba su ba da takamaiman adadin mutanen da hadarin ya rutsa da su ba.

"Abin ba kyan gani" inji Ed Troyar, wani dan sanda mai magana da yawun rundunar yankin da ake kira Pierce.

Ya kara da cewa " a wannan lokacin, babu wanda ya ji ciwo cikin masu tafiya kan titi, wanda suka ji ciwo na cikin jirgin kasa ne kawai, amman ba mu da tabbacin adadinsu."

Hotunan inda abin ya faru, wadanda ‘yan sanda suka raba, sun nuna cunkoson ababan hawa zagaye da wani tarago da ya yi kacakaca.

Sannan wani taragon kuma yana lilo daga kan gadar da hadarin ya faru a tsakanin yankin da ake kira Tacoma and Olympia da babban Birnin na jihar Washington.

Taragon dake lilo
Taragon dake lilo

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG