An Gano Gawar Mutumin Da Ake Zargi Da Harbe Mutane 18 Har Lahira A Jihar Maine

Maine Shooting

Hukumomin jihar sun ce mutunin da ake zargi da yin harbin ya mutu ne sakamakon raunin da ya ji daga harbin bindigar da yayi wa kansa.

Jami’ai sun ce An tsinci gawar Robert Card, wanda suka yi imanin cewa shi ya kai harin harbin da aka yi a jihar Maine da ke arewacin Amurka,.

Michael Sauschuk, kwamishinan kula da lafiyar al’uma na jihar, ya fada a wani taron manema labarai cewa Card ya mutu, ga dukkan alama sakamakon raunin da ya ji daga harbin bindigar da yayi wa kansa.

Gwamnar jihar Janet Mills ta ce an gano gawar Card ne a garin Lisbon Falls, da ke jihar Maine.

Harbin jihar Maine

Hukumomi sun yi ta neman Card dangane da wasu harbe-harbe da aka yi a ranar Larabar da ta gabata a wani wurin wasan bowling da wani wurin cin abinci da shan barasa a garin Lewiston da ke Maine.

Ana kyautata zaton ya kashe mutane 18 tare da raunata wasu 13, ciki har da wasu kurame guda 4.

Da yake fitar da sanarwa da yammacin ranar Alhamis, shugaba Joe Biden ya yaba wa 'yan sanda bisa dagewar da suka yi wajen farautar maharin tsawon kwanaki biyu, ya kuma yi kira ga 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar Republican da su taimaka su bada hadin kai a rage tashin hankalin bindiga.

Bindiga

Dama 'yan Democrat suke goyon bayan a tsaurara matakan mallakar bindiga yayin da 'yan Republican ke nuna damuwa cewa matakan za su saba wa tanadin kundin tsarin mulkin kasar da ya ba Amurkawa 'yancin mallakar bindiga.