Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan Jami’an Tsaro Sun Bazama Neman Mutumin Da Ake Zargi Da Harbe Mutum 18 A Amurka


Yadda jami'an tsaro suke neman maharin ba dare ba rana.
Yadda jami'an tsaro suke neman maharin ba dare ba rana.

An rufe dukkan makarantun gwamnati da ke kusa da Lewinston a ranar Juma’a yayin da hukumomin ke ci gaba da farautar mutumin wanda ake kira Robert Card.

Daruruwan ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaron Amurka a ranar Juma’a na ci gaba da neman mutumin da ake zargi da hannu a mutuwar mutum 18 a jihar Maine da ke gabashin kasar.

Mutumin mai shekaru 40 ya harbe mutanan ne a wani wajen shakatawa da wani gidan shan barasa a birnin Lewiston.

Shugaban ‘yan sandan jihar ta Maine, Kanar William Ross, ya ce mutumin da ake nema mai suna Robert Card “na dauke da makami kuma yana da matukar hadari” saboda haka, duk wanda ya gan shi ya kira ‘yan sanda kada ya tunkare shi.

A ranar Alhamis ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun fi mayar da hankalinsu ne kan wani gidan dan uwan Card inda ake tunanin yana ciki.

An rufe dukkan makarantun gwamnati da ke kusa da Lewinston a ranar Juma’a yayin da hukumomin ke ci gaba da farautar Card.

‘Yan sanda sun ce Card, wanda sojin Amurka ne mai zaman jiran kar-ta-kwana, ya ba da rahoton cewa yana fama da matsalar kwakwalwa.

Card ya shiga wajen shakatawar na Bowling Alley a ranar Laraba ya bude wuta da wata bindiga mai sarrafa kanta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG