An Gano Mutumin Da Ya Harbe Ma'aikatan Wata Jaridar Amurka

‘Yan sanda a jihar Maryland da ke nan Amurka sun gano mutumin da ya kashe mutane biyar a ranar Alhamis a kamfanin jaridar Capital Gazette, da ke yankin Annapolis, dauke da gurneti mai hayaki da bindiga.

Jami’ai sun ce Jarrod Ramos ya sha samun sa’in sa da jaridar Capital Gazette. Hukumomi sun ce harin shiryayye ne, kuma Ramos ya nemo wadanda yake hari kafin ya kashe su. Jami’an tsaro sun isa wurin akan lokaci, amma maharin har ya riga ya kashe ‘yan jarida hudu da wani jami’in kasuwanci.

‘Yan shaidar gani da ido sun shaida cewa maharin ya harba bindiga ta wata kofar gilishi ne a jiya Alhamis din da misalin karfe 3 na rana a gidan jaridar.

Wani dan jarida da ke aiki a lokacin da harbin ya auku, ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, ‘’ yayin da nake boye a karkashin teburi na, inna jin maharbin na harbi tare da karawa bindigarsa lodin harsasai.

Yanzu haka dai Ramos na hannun hukuma tare da gurfanar da shi a gaban kotu da safiyar nan ta Juma’a bisa tuhumarsa da laifuka kamar 5 masu nasaba da kisan kan da ya aikata.