Sassan biyu dai sun gana da mai ba wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, da baiyana cewa masu tada hankali wasu tsiraru ne kawai da a kan samu a kowane addini da kowace kabila da kowace sana’a.
“Fulanin da mu ka sani masu son zaman lafiya ne, amma ba mu san me ya faru a ke samun wasu can daban da ke shiga rigar su, ana kawo matsala ba” inji sakataren kungiyar sarakuna mabiya addinin Kirista Reverend Gbenga Olumuyiwa.
Shugaban kungiyar MIYETTI ALLAH Muhmmad Kiruwa Ardon Zuru, ya ce za su ci gaba da ganawa da kungiyoyi mabanbanta don samun fahimtar juna da dawo da salama mai dorewa.
Janar Monguno, ya nuna gamsuwar gwamnatin Najeriya da wannan yunkuri da kira ga dukkan al’umma su zauna kan teburin shawara wajen samun sulhu.
Monguno, ya jawo ayar nazari ta uban al’ummar Indiya Mahatma Gandhi, da ke cewa in an yanke hukuncin wajen wanda ya cire idon wani a cire na sa, ma’ana ramuwar gaiya to za a iya wayar gari kowa sai ya zama makaho.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5