“Mun samu labarin tabbacin ganin sabon watan Ramadan daga shugabanni da kungiyoyin addinin Musulunci daga ko ina a kasar nan, kuma kwamitocin duba wata sun tantance
Sokoto, Najeriya —
Shugaban Majalisar koli kan lamurran addinin Musulunci, Mai alfarma Muhammad Sa'ad Abubakar, ya umurci Musulmi a Najeriya da su dauki azumi a gobe Alhamis.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne bayan da majalisar ta samu bayanai kan ganin jinjirin watan Ramadan a sassan Najeriya.
“Mun samu labarin tabbacin ganin sabon watan Ramadan daga shugabanni da kungiyoyin addinin Musulunci daga ko ina a kasar nan, kuma kwamitocin duba wata sun tantance.
“Bisa ga haka, gobe Alhamis 23 ga watan Maris, 2023, ya zama daya ga watan Ramadan, wato shekara 1444 bayan bayan hijira.
“Saboda haka, muna kira ga al’umar Musulmi a duk fadin kasar na, da mu tashi da azumi gobe idan Allah Subahanahu wata’ala ya kai mu.” In Muhammad Sa’ad.