An Fitar Da Najeriya A Gasar Cin Kofin Duniya Ta ‘Yan Kasa Da Shekaru 20

'Yan wasan Najeriya (Hoto: Facebook/NFA)

Koriya ta Kudu da Uruguay sun kai zagayen kusa da na karshe a gasar FIFA ta cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 20.

Uruguay ta doke Amurka da ci 2-0 a Santiago del Estero, inda suka mamaye wasan daga farko har karshe kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Ita kuwa Koriya Ta Kudu ta doke Najeriya ne da ci 1-0 bayan da aka kara lokaci.

Yanzu Uruguay za ta fafata da Isra’ila a ranar Alhamis yayin da Koriya ta Kudu kuma za ta gwada kwanjinta da Italiya don neman gurbi a wasan karshe.