Dakarun Sojojin Najeriya sun kwato garin Dikwa bayan da suka fatattaki ‘yan kungiyar Boko Haram, daga garin, inda suka kashe da dama daga cikinsu.
Mataimakin darakta mai hulda da jama’a na runduna ta bakwai na Sojojin Najeriya, dake Maiduguri, Kanal, Tukur Gusau, wanda ya bayana haka ga manema labaru cikin harda wakilin muryar Amurka Haruna Dauda, yace “ Sun tarwatsa ‘yan kungiyar ta Boko Haram, sun kuma kashe mutane ashirin.
Ya kara da cewa sun lalata motocin ‘yan Boko Haram masu dauke da Boma Bomai, da kuma kwato makamai da dama kamar bindigar harbor jirgin sama da bindigogi masu sarrafa kansu da albarusai akwati akwati bacin makama da rundunar suka lalata.
Yace wannan shine karo na farko da Sojojin Najeriya, suka shiga garin Dikwa, yana mai cewa Alhamdulillahi babu Sojan Najeriya, ko daya da aka kashe ko kuma ya samu rauni.
Ya kuma kara da cewa a sanin su a halin yanzu babu wani karamar hukuma da yake hannun ‘yan kungiyar Boko Haram, ya kuma nanata cewar wannan yakin ba wai tsakanin ‘yan Boko Haram da Sojoji bane tsakanin ‘yan Boko Haram da duk ‘yan Najeriya, ne.