A sanarwar da kakakinta Tidjani Abdoulkadri ya gabatar gwamnatin ta Nijer ta fara ne da nuna bacin ranta game da faruwar wannan al’amari da ya yi sanadin mutuwar fararen hula 37 cikinsu har da yara 13 da mata 4 wanda kuma ta dora alhakinsa a wuyan wasu wadanda tace sun ketaro ne daga wata kasa makwafciya.
Gwamnatin ta Nijer ta ayyana zaman makokin kwanaki 2 daga yau laraba a fadin kasar inda aka sassafta tutoci domin nuna alhini akan kashe kashen na kauyen Darey Dey wanda shine karo na 3 dake rutsawa da fararen hula a gonakinsu a shekarar nan ta 2021.
Kungiyoyin kare hakkin jama’a ko kuma Voix des sans Voix ta bakin Alhaji Nasssirou, shugaban kungiyar sun yaba da matakin gwamnatin domin a cewarsu abu ne da zai sanyaya zuciyar dangin wadanda abin ya rutsa da su to amma kuma suna masu kira ga hukumomi su dauki matakai donganin talakka ya sami walwala a duk inda yake a wannan kasa..
Sanarwar gwamnatin ta Nijer ta kara da cewa tuni aka tsaurara matakan tsaro a yankin da abin ya faru yayinda a daya bangare aka kaddamar da bincike domin zakulo masu hannu a wannan danyen aiki domin gurfanar da su a gaban koliya. yankin Tilabery mai makwaftaka da kasashen Mali ya fada cikin yanayin tabarbarewar tsaro shekaru 2 bayan tarewar ‘yan ta’adda a arewacin Mali da Burkina Faso lamarin da ya samo asali daga faduwar gwamnatin Kaddafi a 2011.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5