An Fara Shirye-Shiryen Watan Ramadan

A kowacce shekara mata kan yi canje-canje domain gabatowar watan ramadana. Dandalin VOA ya gana da wasu mata a kwarayar Kano dangane da irin shirye-shiryen da suke yi na gabatowar watan ramadan.

Wasu daga cikin matam sun fada wa wakiliyar Dandalin VOA, Baraka Bashir irin abubuwan da suke saye kafin a fara azumi, kamar su Kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi.

Amma kuma Matan sun koka Akan cewa har yanzu babu rangwame a wasu kayayyakin haka kuma babu wani kari. Wasu matan kuma sun shaida cewa akwai rahusa akan wasu kayayyakin.

Ga rahoton Baraka Bashir.