Matakin baya bayanan shine na horas da jami'an tsaro na banga da yake wasu Jihohi sun haramta ayukkan ‘yan sa kai a Jihohin su.
Matsalolin rashin tsaro dai a Najeriya musamman a yankin arewa suna son furce sanin kowa domin an yita daukar matakan magance su amma an kasa samun bakin zaren shawo kan matsalar.
‘Yan banga wadanda suna cikin wadanda ake amfani dasu wajen samar da tsaro suna bada gudunmuwa ga lamarin tsaro kamar yadda wani dan banga a Sakkwato ya damke wasu da ake tunanin 'yan fashin daji ne.
Abubakar Muhammad AH sakataren kungiyar banga ne na jihar Sakkwato ya bayyana yadda lamarin ya faru.
Akan irin wannan gudunmuwar da suke bayarwa ne, ya sa rundunar ‘yan sanda ta dauki dawainiyar horas da ‘yan banga dubarun aikin samar da tsaro inda bayan sun kammala karbar horan kwamandan makarantar horas da 'yan sanda da ke Sakkwato ya gargade su.
Yanzu da yake an haramta ayukkan ‘yan sa kai a wasu jihohi akwai yuwuwar nauyi zai kara yawa ga ‘yan banga amma duk da haka sun nuna shirinsu na yin aiki tukuru.
Sai dai kuma akwai wata fargaba da sakataren kungiyar na jihar Sakkwato ya ce suna fuskanta musamman a haujin ‘yan siyasa.
Fatan jama'a dai ba zai wuce ganin an kawo karshen wadannan matsalolin na rashin tsaro ba, abin jira a gani tasirin da horas da 'yan bangar zai yi domin a watannin baya ma an horas da ‘yan sandan al'umma amma dai kawo yanzu jama'a basu shaidi tasirin da suka yi musamman wajen samar da tsaro.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5