Kwamitin ya ji cewa rikicin ya fi ta'azara a lokacin damina, to sai dai Shugaban Kwamitin ya nuna bacin ran sa kan yadda jami'an tsaro ba su amsa gaiyyata ba a zaman sauraren ba'asin.
Wannan Kwamiti na wucin gadi da Majalisar wakilai ta dora wa alhakin tattaunawa da wadanda batun rikicin Fulani Makiyaya da Manoman ya shafa ya nuna rashin jin dadin sa kan yadda wasu Jami'an tsaro da aka gayyato zuwa taron suka ki amsa gayyata zuwa taron jin ra'ayoyin.
Shugaban Kwamitin Onorabil Aliyu Bappah Misau ne ya bayyana rashin jin dadin kwamitin. Bappah ya ce ba su nuna dattaku ba, kuma basu mutunta Majalisar ba balle Kwamitin. Bappah ya ce lallai Majalisa da Kwamiti ba su ji dadi ba.
Amma wanda ya gabatar da Kuduri a Majalisar kan batun rikicin Fulani Makiyaya da Manoma Onorabil Inuwa Garba wanda shi ne yake wakiltan yankin Yamaltu Deba ta Jihar Gombe ya jinjina wa kokarin da mai ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro Mallam Nuhu Ribadu yake yi kan wannan batu. Inda ya jaddada kudurin kwamitin da ma Majalisar cewa za su yi dukan abinda ya dace na karbar gudumawar kowa domin daidaita al'amura.
Inuwa yace wannan Kwamiti zai sake rubuta wa jami'an tsaron nan gaba, kuma za su dauki mataki ko da za su rubuta wa Shugaban kasa takarda ne akan haka tare da bada sunayen wadanda abin ya shafa domin a nuna wadanda ba sa bada hadin kai kan al'amuran tsaro a kasar. Inuwa ya ce wanna ya nuna cewa ba aikin kasa suke yi ba sai aikin kan su.
A nasu bangaren Shugaban Kungiyar Fulani Mikiyaya ta Kullen Allah Khalid Mohammed Bello ya bada shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalar inda ya ce idan ana so a shawo kan wadannan matsaloli da ke faruwa tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma to a dawo da burtaloli da ka toshe.
Shugaban Kwamitin Aliyu Bappah Misau ya kara da bayyana cewa matsayin jami'an tsaro wajen kwantar da tarzona ko tashin hankali abu ne muhimmin gaske saboda su kadai dokar Kasa ta dora wa alhakin aiwatar da duk wani matsayi da aka zartar don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma baki daya.
Abinda ya dauki hankali shi ne cewa wakilin Mai ba Shugaban Kasa shawara Kan harkar tsaro, da jami'an rundunar tsaron ta farin Kaya, Sibil difens ne suka halarci taron.
Kwamitin ya ce zai kai ziyarar gani da ido a wannan yanki na Yamaltu Deba ta Jihar Gombe, tare da dukan sassa da irin wannan rikici ya ritsa da su.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5