Sabuwar dokar za ta taimaka wajen rage cunkoson fursunoni, amma sun nanata cewa, akwai bukatar masu ruwa da tsaki su kara kaimi ta wannan fuska.
Kididdiga daga ma’aikatar kula da lamuran cikin gida ta Najeriya ta nuna yawan daurarrun dake cibiyoyin gyaran hali ko gidajen yari daban-daban a fadin kasar ya zarce ka’ida da dubu 11500, lamarin dake tabbatar da yanayin cunkoso a gidajen yarin kasar.
Yanzu haka dai gwamnatin kasar na gina sabon gidan yari a Kano da zai dauki yawan daurarru dubu uku, wanda ake sa ran kammalawa nan ba da jimawa ba.
Kakakin shiyyar Kano na hukumar kula da gidajen gyaran hali da aka fi sani da gidajen yari ta Najeriya DSP Misbahu Lawan Kofar Nasarawa ya yi tsokaci kan matakan doka na rage cunkoson daurarru.
Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya biya basussu da tara ga wasu daurarru su 38 dake gidajen gyaran hali na Kurmawa da Goron Dutse a Kano, jimlar kudi kusan miliyan 22.
Ko a kwanakin baya gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi amfani da hurumin da doka ta bashi wajen yin afuwa ga wasu daurarru masu kananan laifuka, kamar yadda babban jojin Kano kanyi amfani da tasa damar ya yi irin wannan afuwa ga dauarrun daga lokaci zuwa lokaci.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5