Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Edward Egbuka ne ya shaida wa manema labarai bayan wani taron gaggawa da gwamnatin jihar ta kira don dakile matsalolin tsaro da suka kazanta a kananan hukumomin Bassa da Riyom a jihar.
A cewar Egbuka, tuni sun ruga sun baza jami'ansu a yankunan da rikicin ya faru domin kaucewa yaduwarsa a sassan jihar.
Kwamishinan yada labarai da sadarwa a jihar Filato, Mr. Dan Manjang ya ce gwamnati na iya kokarinta wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.
Ya kara da cewa ya rage wa wadanda ke da hurumin aiwatar da hukunci ne su aiwatar kan wadanda aka kama ake tuhuma da haddasa rikicin.
"Akwai wadanda ma har an kama, an kai su gaban kuliya, an ba da belinsu, kinsan yadda harkokin dokokin namu suke a Najeriya, ba ka da hurumin ka ajiye mutum na wasu kwanaki, sai ka ga kungiyoyi daban-daban suna harararka" In ji Manjang.
"Har yanzu mutanen da ake kama su da irin wadannan dabi'u ba a hukukta su ba, wannan alhaki ya hataya a wuyan 'yan sanda da kotuna." ya kara da cewa.
Rikicin na kwanan nan tsakanin Fulani da kabilar Irigwe ya yi sanadin rasa rayuka, kone gidaje, lalata amfanin gonaki da dabbobi.
Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji: