An Dorawa Rasha Laifin Kakkabo Jirgin Malaysia Mai Lamba MH17

Jirgin Malaysia Mai Lamba MH17

Kasashen Netherlands da Australia sun ce Rasha suke dorawa laifi kuma zasu nemi diyya akan fadowar jirgin saman nan na Malaysia mai lamba MH17 da ya fado a yankin gabascin Ukraine da ake yaki a cikinsa shekaru hudu da suka gabata, har dukkan mutane 298 da ma’aikatan jirgin suka hallaka.

Da yake magana da manema labarai a Hague, ministan harakokin wajen Netherlands, Stef Blok ya ce, “yanzu an tabbatar ba tare da wata shakka ba, cewa akwai alaka tsakanin rokar nan da ta tarwatsa jirgin saman MH17 da kuma rundunar sojan Rasha.”

A jiya Alhamis ne dai masu bincike suka yanke hukuncin cewa makami mai linzamin da ya kakkabo jirgin saman, wanda yake kan hanyarsa daga Amsterdam zuwa birnin Kuala Lumpur, ya samo asali ne daga wata bataliyar soja dake a can Rasha.

Sai dai Rasha ta musanta zargin a yau Juma’a, inda take cewa hukumomin na Netherlands basu gabatar da wata kwakwarrar sheda ba dake nuna gaskiyar zargin da suke, illa kawai suna neman cimma nasu burin.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce tana karfafa zaton ‘yantawayen Ukraine ne suka harbi jirgin.