Mutane a kalla 6 suka mutu bayan da bam ya tashi cikin wata mota a tsakiyar birnin Benghazi dake gabashin kasar Libiya da daren jiya Alhamis, kamar yadda mazauna wurin suka gaya ma kafar labarai ta Reuters.
Bam din ya tashi ne daura da otal din Tibesti, wanda shi ne ya fi girma a birnin. Motocin daukar majinyata sun yi ta rugawa zuwa wurin. To amma nan take dai ba a kara wani bayani ba.
Benghazi, birni na biyu a girma a kasar Libiya, na karkashin ikon dakarun da suke kiran kansu Askarawan Kishin Kasar Libiya (LNA a takaice) ne, wadanda su ne su ka fi karfi a gabashin Libiyar kuma Khalifa Haftar ne ke jagorantarsu.
Askarawan na LNA sun sha fafatawa da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayin addini, ciki har da masu alaka da ISIS da al-Qaida, da kuma sauran kungiyoyin da ke adawa da su har zuwa wajajen karshen bara, a wannan birni mai tashar jirgin ruwa a gabar Tekun Bahar Rum.
Tun bayan nan matakan tsaro sun inganta, to amma hare-haren bam da aka kai kan wasu masallatai biyu a farkon wannan shekarar sun yi sanadin mutuwar mutane akalla 35.
Facebook Forum