Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Congo Ta Yi Anfani Da Darusan Da Ta Koya Wajen Dakile Yaduwar Ebola


Ma'aikatan hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) suna gyara wurin bada allurar rigakafi da warkar da cutar ebola a Congo
Ma'aikatan hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) suna gyara wurin bada allurar rigakafi da warkar da cutar ebola a Congo

A wannan karon mahukumtan kasar Congo sun yi anfani da darusan da suka koya can baya wajen saurin dakile yaduwar cutar ebola

A lokacinda annobar zazzabin Ebola ta barke a Afrika ta yamma a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, babu wanda yake cikin shirin ko ta kwana akan aukuwar wannan al'amari.

Alluran rigakafin da ake kokarin kirkirowa tun lokacinda aka samu bular annobar zazzabin a shekara ta dubu biyu da goma sha uku tana kasa tana dabo.

Gwamnatoci suna tafiyar hawainiya wajen daukan matakai ko kuma kasa sanin barazana ko kuma hatsarin dake tattare da bular annobar zazzabin.

Su kuma jami'an kiwon lafiya sai suka tsinci kansu cikin tsaka mai wuya wajen bada jinya.

A saboda haka a lokacinda aka samu damar shawo kan matsalar a shekara ta dubu biyu da goma sha shidda fiye da mutane dubu goma sha daya da dari uku sun mutu a kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo a saboda wannan cuta kuma ta lakume fiye da dala biliyan hudu.

A wannan karon a lokacinda aka samu labarin yiwuwar barkewar annobar ebola a wani kauyen jamhuriyar Congo a ranar takwas ga wannan wata na Mayu, cikin kwanaki biyu kasar ta tura masana zuwa yankin. A takaice nan da nan aka fara daukan matakan dakile yaduwar wannan annoba.

Domin kuwa anyi amfani da darusan da aka koya a baya wajen daukan matakan dakile yaduwar cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG