Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Afirka ta Tsakiya Ya Sa Dubban 'Yan Kasar Gudun Hijira Zuwa Kamaru


Mata da yara dake tserewa daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Mata da yara dake tserewa daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Har yanzu ana ci gabada rikicin addini da na kabilanci a kasar Afirka ta Tsakiya wanda ya tilastawa dubban 'yan kasar yin gudun hijira zuwa kasar Kamaru tare da haddasa yawan mutuwar yara 'yan kasa da shekaru biyar

Dubun bubatan jamaa ne ke tserewa daga jamhuriyar Arewa ta Tsakiya wurrin da ake tashin hankali.

Kuma Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta ce da yawan wadannan mutanen suna fama dakarancin taimakon kayayyakin jin kai.

Domin cimma bukatun wadannan mutanen MDD ta ce tana bukatar a kalla dala miliyan 515 wanda ta kaddamar a cikin watan Janairu domin daukar dawainiyar wadannan mutanen amma kashi goma kawai ta iya daukar nauyin su daga cikin adadin jamaar..

Wakilin wannan gidan Radiyon mai aiko da rahotanni daga kasar Kamaru Edwin Moki Kindezeka ya bayyana halin da ‘yan gudun hijirar ke isowa kasar ta Kamaru a gabashin garin Garoua Boulai.

Yanzu haka dai daruruwan yan kasar jamhuriyar Africa ta Tsakiya suke wakar lale marhabin ga ‘yan uwansu da suka iso bakin iyakar garin Gauroua Boulai dake iyaka ajamhuriyar Kamaru.

Wannan wurin ne ‘yan kasar ta Jamhuriyar Africa ta Tsakiya suka tarbi ‘yan uwansu har su 30 wadanda suka tsallako suke shigowa kasar ta Kamaru a cikin wannan satin.

Wannan tabi’ar tarbon mutane daga jamhuriyar Africa ta Tsakiya dai ya zame wata tabiar da suke gudanarwa a sati-sati, inda suke hadewa da ‘yan uwan su dama iyalan su da suka rabu dasu can kasar ko kuma wasu suka yo gaba.

Daga cikin wadannan sabbin zuwan ko da suka tsere daga kasar tasu zuwa jamhuriyar Kamaru har da wani dan taliki mai suna Piera Magnou dan shekaru 37.

Yace shi da iyalan sa suna cikin wadanda ake yunkurin kai ma hari, kuma Sojoji ne suke auna shi da iyalan sa, wadanda ke harbin kan mai uwa da wabi kuma suna bi gida-gida suna kona gidajen jama’a musammam a babban birnin kasar Bangui, yace wannan kuma ya faru ne sati biyu da suka gabata.

Yace a cikin watan Oktoban shekarar 2017 ne shi da matar sa da ‘ya ‘yansa biyu suka dawo daga kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo inda suka tafi gudun hijira amma kuma suka dawo gida Jamhuriyar Arewa ta Tsakiya suka samu wuri tsakiyar musulmai suka zauna suna kyautata zaton cewa an samu zamanlafiya.

Yace anci gaba da mummunar fada a kasar sa tsakanin Musulmai yan Saleka dake fada da kuma Kirista masu kin jinin wannan kungiyar ta ‘yan saleka dama wani bangare na al’ummar kasar. Ya ci gaba da cewa wannan zaman dar-dar din ne basu fatan ganin sun ci gaba da zama a cikinsa abinda ya sa suka arce ke nan domin su tsira da ransu, kuma suna jiran tawagar samar da zaman lafiya ta MDD ta kammala aikinta da take jin ya dace domin ganin an samar da zaman lafiya a wannan kasar.

Rikici dai ya barke ne a kasar ta Jamhuriyar Africa ta Tsakiya lokacinda aka kifar da dadadden shugaban kasar Francois Bozize a shekarar 2013, kuma wadanda suka jagoranci wannan kifar da gwamnatin yawancin su Musulmai ne ‘yan tawaye da ake kira Saleka.

Wannan fa ya sa su kuma sojojin sa kai wadanda galibi mabiya addinin kirista ne suka nemi mayar da martanin wannan kifar da gwamnati da musulmai ‘yan Saleka suka yi, wannan ne fa ya haifar da mummunar fada a kasar kawo yanzu.

Sai dai a cikin watan fabarairu na shekarar 2016 Faustin-Achange Touadera, bayan an zabe shi shugaban kasa yayi alkawarin samar da zaman lafiya.

Amma har yanzu lamarin yaci tura domin ko ministan ayyukan jin kai na kasar Virginie Baikou ta ziyarci Cameroon a cikin satin data gabata tana cewa har yanzu ana fada a kasar ta Jamhuriyar Africa ta Tsakiya domin ko abu ne mawuyaci ace an kawo bangarorin biyu wuri guda domin a zauna har a yi sulhu.

Ta ce “babbar matsalar da yanzu muke fuskanta ita ce yadda makamai ke gilmayya tsakanin jama a, abinda ya sa ya zame wajibi a ilmantar da yara matasa game da illar ta’addanci a ganar dasu cewa yanzu sun kai munzilin da zasu ciyar da kai gaba ta yin aikitukuru amma ba ta kashe junansu ba.

Sai dai mai jagorantar aikin samar da zaman lafiya na MDD a kasar Najad Rochidi ta ce mutanen dake bukatar taimakon gaggawa sun karu a kasar hakan ko ya biyo bayan sake barkewar tarzoma ne.

Kashi 25 cikin dari na wani bangare na daukacin al’ummar kasar suna cikin wani halin kunci da damuwa wanda hakan zai sa a samu saukin shawo kansu su shiga aikin ta’addanci.

Yanzu haka dai yara kashi 18 yan kasa da shekaru 5 a kasar sai mutuwa suke yi, wannan yana nufin kashi 18 na mayan goben kasar ba a basu damar su yi rayuwa ba tare samun damar bada nasu irin gudummawar ciyar da kasar gaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG