A wani shiri na samarda tsaro ga al’umar Maiduguri, da kewaye rundunar 'yan sandan jihar ta bada sanarwar takaita zirga zirgar ababen hawa alokacin da za a gudanar da Sallar Eidi.
Sanarwar dake dauke da sa hannun kakakin rudunar ‘yan Sandan jihar DSP, Victor Isoko, yace za a takaita zirga zirgan ne saboda kare lafiya da dukiyar jama’a wanda ma zai hada da motocin hawa da Babura masu kafa uku da ake kira keke Napep ko kuma a daidaita sahu har ma da dabbobi da ake amfani dasu wajen zirga zirga.
DSP Isoko, yace wannan mataki da aka dauka na takaita zirga zirgan zai shafi kananan hukumomin Maiduguri da Jere ne kawai wanda kuma an yi hakan ne domin tabbatar da cewa an gudanar da Sallar Eidi lafiya batare da samun wani matsalla ba.
Kakakin ya kuna roki jama’a da suyi hakuri da wannan mataki da rundunar ‘yan Sandan ta dauka, yace an dauki matakin ne ba dan a musgunawa kowa ba amma domin tabbatar matakan tsaro.
Tun dai lokacin da aka fara yakin da ‘yan Boko Haram, kusan shekaru bakwai kennan akan dakatar da zirga zirgan ababen hawa a lokutan bukukuwan Sallah, duk irin wadanna matakan an dauka ne saboda tabbatar da cewa an gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.
Your browser doesn’t support HTML5