Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiya da Wasu Kasashen Larabawa Sun Bukaci Qatar Ta Rufe Gidan Talibijan Na Al-Jazeera


Ma'aikata agidan Talabijin Na Al-Jazeera Suna Gudanar Da Aiki Dakin.
Ma'aikata agidan Talabijin Na Al-Jazeera Suna Gudanar Da Aiki Dakin.

Kasashen Larabawa hudu da suka yanke huldar diflomasiyya da Qatar sun bada jerin sharuddan da suke bukata Qatar ta cika.

Saudiyya da sauran kasashen larabawa hudu da suka tsinke huldar diplomasiya da kasar Qatar bayan da suka zargeta da bada goyon baya ga kungiyoyin ‘yan ta’adda, sun mikawa ‘kasar Qatar din jerin bukatun abubuwan da suke so ta aiwatar kafin su shirya da ita.

‘Kasar Kuwait, wadda itace mai shiga tsakanin Qatar da kasashen larabawan da suka hada da Saudi Arabia da Bahrain da Daular Larabawa da kuma Masar, itace ta hannunta wa Qatar bukatun da suka hada da mai neman Qatar ta yanke hulda da Iran ta kuma dakatar da duk wani huldar diplomasiyya, ta kuma rufe kamfanin labarai na al-Jazeera da dukkan tashoshin dake karkashinsa.

Bukatun sun kuma nemi Qatar ta yanke hulda da duk kungiyoyin ta’addanci, musamman ma kungiyar, 'Yanuwa Musulmi ko Muslim Brotherhood da ISIL da al-Qaida da kuma kungiyar Hezbollah ta Lebanon.

Sun kuma bukaci Qatar cikin gaggawa ta sallami sojojin Turkiyya da yanzu haka ke cikin ‘kasarta, da duk wani abu da ya hada da dakarun Turkiyya a cikin Qatar.

Kasashen Larabawan dai sun baiwa Qatar wa’adin kwanaki goma da ta amince da wadannan bukatu, sai dai kuma basu bayyana abinda zai faru ba idan har Qatar bata amince da bukatun ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG