Nijar Ta Dage Ranar Komawa Makarantu Saboda Ambaliyar Ruwa

Ambaliyar Ruwa

Ambaliyar da ake fama da ita sakamakon ruwan da ake tafkawa a jamhuriyar Nijar ya yi sanadin daga ranar komawar dalibai ajin karatu zuwa 28 ga watan Oktoban dake tafe a maimakon 1 ga wata.

Dubban dakunan karatu ne suka ruguje sanadiyar ambaliya yayin da a wasu yankunan mutanen da wannan iftila’i ya ruguza gidajensu suka nemi mafaka a makarantun boko, dalili da kenan hukumomin kasar suka yanke shawarar daga ranar sake bude makarantu zuwa karshen wata.

Kamar yadda a farkon shekarar nan ta 2024 masana suka yi hasashen yiwuwar saukar ruwan saman da ka iya haddasa mummunar ambaliya haka abin ya wakana a illahirin yankunan kasar Nijar inda a yanzu haka ake ci gaba da tafka ruwa kamar da bakin kwarya.

Lamari ya janyo asarar rayukan daruruwan mutane da rugujewar dubban gidaje da dakunan karatu, a wani lokacin da ya rage mako guda a kammala babban hutun ‘yan makaranta, dalilin da kenan gwamnati ta daga ranar zuwa 28 ga watan Oktoba. Matakin da kungiyoyin malaman makaranta irinsu SYNAFCES suka ce ya yi dai-dai inji sakatarenta Jariri Labo Saidou.

Wata matsalar ta daban da ta haddasa cikas a shirin komawa ajin karatun shekarar 2024-2025 shine yadda a yanzu haka mutanen da iftila’in ambaliyar ya raba da mahallansa ke samun mafaka a dakunan karatu.

Shugaban kungiyar COADD mai fafutikar samar da ilimi mai inganci Dr. Amadou Roufai Lawan Salao na cewa daga ranar shine mafi a’ala idan aka yi la’akari da yanayin da ake ciki.

To sai dai wasu ‘yan kasa sun gargadi gwamnatin akan bukatar daukan wasu karin matakai don cike gibin da matakin daga ranar komawar karatu zai haddasa.

Mutane sama da million daya ne ambaliyar ruwa ta raba da matsugunansu a bana kuma a cewar hukumomi daga cikinsu sama da kashi 90% ne a ka bai wa tallafi a matsayin agajin gaugawa da suka hada da cimaka da wasu kayayakin bukatu.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

An Dage Ranar Komawar Dalibai Makaranta A Nijar Sakamakon Ambaliyar Ruwa