An Daga Wasannin Lig Lig Na Najeriya Zuwa Laraba

Magoya bayan Super Eagles na Najeriya

An daga wasannin Firimiya Lig na Najeriya da za’ayi na wannan makon zuwa sati mai zuwa, an dai mai da wasan ranar Laraba 21 ga watan Oktoba, a dalilin wasan da za’ayi tsakanin Super Eagles da Burkina Faso.

Shawarar yin hakan ta zo ne a dalilin wasu kungiyoyin zasu rasa wasu ‘yan wasansu masu kyau domin wasan kasa.

An dai sanar da kungiyoyin cewa wasannin su na karshen mako kamar yadda suka saba yi an matsar da shi zuwa ranar Laraba, saboda wannan wasa mai muhimmanci dake tafe.

Najeriya ce dai zata karbi bakuncin wannan wasan karo na farko da za’ayi a jihar Port Hourcourt, kafin komawa Ouagadougou domin fafatawa a karo na biyu mako mai zuwa.

Duk wanda ya samu nasarar wannan wasa biyu da zasuyi to zai sami shiga wasan CHAIN da za’ayi shekara mai zuwa a Rwanda.