Shugaban kwamitin Majalisar Wakilan Amurka kan bayanan sirri, dan jam’iyyar Demokrat, ya ce sun cimma matsaya don jin ta bakin wani mai kwarmato wanda korafin da ya yi ya janyo kafa kwamitin binciken yiwuwar tsige Shugaban Amurka Donald Trump.
“Muna daukar dukan matakan da za mu iya daukawa don mu samu damar sauraron ba'asin ta yadda za a sakaya sunan mai kwarmaton,” abin da Adam Schiff ya fada a cikin shirin gidan talabijin na ABC News mai suna “This Week” kenan. "Ganin yadda Shugaban kasa ke barazana, ka na iya gane misalin irin damuwar da ke akwai ta tsaro."
Sai dai mai kwarmaton ya yi zargin cewa Shugaba Trump, a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da sabon Shugaban kasar Ukraine a ranar 25 ga watan Yuli, ya yi kokarin neman taimako ta wajen tono bayanan da za su aibata tsohon Mataikin Shugaban kasa Joe Biden da dansa Hunter da zai yi wa damar da Biden yake da ita ta samun nasara jam’iyyar Demokrat ta tsayar da shi takara da zai kalubalanci Trump a zaben shakarar 2020.