Wakilin Shugaban Amurka Donald Trump na musamman kan Ukraine, ya yi murabus daga mukaminsa, kamar yadda kafofin yada labaran Amurka suka ruwaito, wadanda suka samo labarin daga wasu majiyoyi da ke da masaniya kan batun.
Rahotanni sun ce, Kurt Volker ya ajiye aikin nasa ne, bayan wata ganawa da ya yi da Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, sai dai ma’aikatar harkokin wajen, ba ta mayar da martani nan take ba a lokacin da aka tuntube ta domin jin ta bakinta.
Shi dai Volker, an ambaci sunansa a korafin da aka fitar, wanda wani da ba a san ko waye ba, ya ta-da likin da ya kai ga aka kaddamar da bincike da mai yiwuwa ya kai ga tsige Shugaba Trump.
A cikin korafin, an nuna cewa Volker shi ya hada ganawar da aka yi tsakanin lauyan Trump na kansa Rudy Juliani, da jami’an gwamnatin Ukraine
Ana dai zargin Shugaba Trump da sa shugaban Ukraine Velenskiy, ya kaddamar da bincike kan dan tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, Hunter, wanda da shi ake tunanin zai kara a zaben 2020, da nufin bankado wani abu da zai bata mai suna.
Sai dai Trump ya musanta yin ba daidai, ya kuma yi ta Allah wadai da masu kambama wannan batu.