An Ceto Mutane 5, Tare Da Gano Gawawwaki 9 Daga Hatsarin Kwale-Kwalen Zamfara

  • VOA Hausa

Hatsarin Jirgin Ruwan a Gummi

A cewar NEMA, kawo yanzu an gano gawawwakin fasinjoji 9, sannan ana cigaba da gudanar da aikin ceto.

An yi nasarar ceto mutane 5 tare da gano gawawwaki 9 daga hatsarin kwale-kwalen daya faru a lahadin data gabata a kogin Mashayar Yandaga dake karamar hukumar Gumin jihar Zamfara.

Sanarwar da kakakin hukumar bada agajin gaggawar Najeriya (NEMA), Manzo Ezekiel, ya fitar a yau Talata tace kwale-kwalen daya gamu da hatsarin na dauke ne da fiye da fasinjoji 40, galibinsu manoma da matukansa lokacin da ya kife sakamakon lodi fiye da kima da karfin igiyar ruwa.

An fidda sanarwar ne bayan da ofishin NEMA na Sokoto da takwaransa na Zamfara da hukumomin karamar hukumar Gumi da shugabannin al’umma da jami’an kungiyar bada agaji ta Red Cross da sauran masu ruwa da tsaki sun yi nazarin yadda iftila’in ya afku.

Ku Duba Wannan Ma Mutane 35 Sun Bace Cikin Ruwa A Zamfara

Bayan afkuwar hatsarin ne aka tattaro masu aikin ceto da suka kunshi gwanayen ninkayar yankin da masunta kuma suka yi nasarar ceto mutane 5 a raye.

A cewar NEMA, kawo yanzu an gano gawawwakin fasinjoji 9, sannan ana cigaba da gudanar da aikin ceto.