A wata sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar ta ce ‘yan Boko Haram din da aka kama ‘yan kasar Chadi ne, wadanda aka cafke unguwar Arawa da Mallam Inna a garin Gombe, mai makwabtaka da jahohin Borno da Yobe a shiyyar Arewa maso
Gabashin Najeriya.
Da yake yiwa sashen Hausa na Muryar ‘karin haske, daraktan labarai a hedikwatar sojin Najeriya, Birgediya Sani Usman Kukasheka, yace a wani hadin aikin hadin gwiwa tsakanin rundunar soja da hukumar tsaro ta ‘kasa DSS, sun gudanar da wani aiki tare har ta kai ga cafke wasu ‘yan Boko Haram su uku.
Kukasheka, ya ce an tabbatar da cewa mutanen uku da aka kama ‘yan kungiyar Boko Haram kuma ‘yan ‘kasar Chadi ne da suke shigowa Najeriya su yi barna, haka kuma binciken farko da aka gudanar an gano cewa suna cikin bangaren kungiyar Al-Barnawi. A lokacin da jami’ai suka yi kokarin cafke ‘daya daga cikin mutanen mai suna Bilal Mohammed Umar, wanda jami’an suka harbeshi a ‘kafa kuma yanzu haka yana asibiti ana bashi magani.
An dai kama mutanen da ake zargin ‘yan Boko Haram ne da sinadaran hada bama bamai, wadanda ake kyautata zaton suna da niyyar kai wani mugun hare ne a garin Gombe ko wani bangare na ‘kasar.
A cewar tsohon gwamnan mulkin soja na jahar Kano, Kanal Aminu Isah Kwantagora, yace batun ‘yan Boko Haram har yanzu da sauran rina a kaba. Inda yayi kira ga jama’a da suyi taka tsan-tsan wajen lura da abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5