Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gombe: Ce-ce Ku-ce Ya Biyo Bayan Zaben Kanana Hukumomi


Zaben ya fuskanci matsalar rashin ganin kayan aikin zabe a tashoshin zabe wanda hakan ya jawo korafi daga jam’iyyar APC.

Wani jami’in zabe Musa Muhammad, a Buhari Estate, ya ce an gudanar da zabe lafiya kuma kowa ya zabi abinda yake so.

Wakilin jam’iyyar APC, Sardaunan Matasa, ya ce jama’a da dama sun yaba da yadda aka gudanar da zaben yankinsu, a nasu bangaren ‘yan jam’iyyar PDP, wanda Yakubu Zakari, ke wakilta shima ya ce zaben ya gudana kamar yadda aka tsara.

Abdulkadir Muhammad Bello, dan takarar shugaban karamar hukumar Gombe, a karkashin inuwar jam’iyyar APC, ya shaidawa wakilin Muryar Amurka Muhammad Abdulwahab, cewa zabe dai a tashi mazabar bai gudana ba.

Kuma duk kokarin da ya yi domin jin ta bakin hukumar zaben jihar ya cutura.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG