Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi

Your browser doesn’t support HTML5

An kama wani dan Najeriya da ke jagorantar kungiyar da ke neman  ballewar yankin  kudu maso gabashin Najeriya kuma za a gurfanar da shi a Abuja, babban birnin kasar, in ji hukumomi.

An kama wani dan Najeriya da ke jagorantar kungiyar da ke neman ballewar yankin kudu maso gabashin Najeriya kuma za a gurfanar da shi a Abuja, babban birnin kasar, in ji hukumomi.

An kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, kuma an dawo da shi Najeriya daga wata kasar da ba a bayyana ba don fuskantar shari'a, in ji Ministan Shari'a, Abubakar Malami.

Ana sa ran zai bayyana a gaban kotu a watan gobe.

Kanu ya tsere daga Najeriya ne a shekarar 2017.

Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Abubakar Malami, Biafra, Biyafara IPOB, Abuja, Nigeria, da Najeriya.