Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan IPOB Da Wasu Bata-Gari


Sojojin Najeriya a wani aikin sintiri da suka yi (Facebook/ Nigerian Army)
Sojojin Najeriya a wani aikin sintiri da suka yi (Facebook/ Nigerian Army)

Bayan da wani bidiyo mai zargin sojoji da aikata sababi da kone kone a jihar Imo ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta tun daga jiya Litini, rundunar sojin Najeriya ta yi wuf ta karyata abin da ta kira farfagandar masu aikai aika da magoya bayansu.

A faifan bidiyon ana iya jin wani mutum na cewa, “Sojojin Najeriya sun shigo sun kona ko’ina. Wai me ya ya faru; wai me ya faru …?

Kan haka ne Mukaddashin Mataimakin Jami’in Hulda da Jama’a na Runduna ta 82 ta Sojin Najeriya, Manjo Abubakar Abdullahi, ya mai da martani yayin da Muryar Amurka ta tuntube shi. Ya ce sam ba haka abin ya ke ba. Hasali ma, ‘yan tsagaran ne su ka tafka ta’asa; su dai sojoji dauki su ka kai.

Tun da farko, a wata takardar martani, Rundunar sojin Najeriyar ta ce dakarun sintiri da ke gudanar da wani atisaye sun fatattaki ‘yan kungiyar IPOB/ESN da ke kone kone yayin da su ke kokarin tilasta wa mutane aiki da haramtacciyar dokar hana fita wadda haramtacciyar kungiyar ta kafa wa al’ummar Awo-Mmamma ta Karamar Hukumar Oru East da ke jihar Imo jiya, 22 ga watan nan na Nuwamba. Takardar na dauke da sa hannun Mukaddashin Mataimakin Jami’in Hulda da Jama’a na Runduna ta 82 ta Sojin Najeriya, Manjo Abubakar Abdullahi.

A wani yinkuri na tilasta ma mazauna yankin yin biyayya da haramtacciyar dokar, ‘yan tsageran IPOB/ESN sun shiga kuntata ma mutane masu zirga zirga, da hantararsu da ma bugu, yayin da su ke kokarin nemar halaliyarsu, a cewar sanarwar. Ta kara da cewa har ‘yan tsageran sun shiga kone konen wuraren kasuwanci da gidajen mutane a wajejen shataletalen babbar hanyar Owerri da Onitsha (Anacha) a matsayin martani ga wadanda su ka ki yin biyayya da haramtacciyar dokarsu din.

Sanarwar ta ce dakarun sintiri sun ruga kai dauki bayan da su ka samu kiran neman taimako daga masu shaguna da direbobin motoci a daidai lokacin da ‘yan tsageran su ka kona wata motar ‘yan kasuwa da ta nufi Anacha. Nan da nan dakarun sintirin su ka shiga fafatawa da musayar wuta da ‘yan tsageran. Dakarun sintirin sun fatattaki ‘yan tsageran har kowannensu ya yi ta kansa, a cewar sanarwar.

Dakarun sintirin sun fafari ‘yan tsageran har zuwa mabuyarsu da ke Akatta a Karamar Hukumar Oru East, inda aka hallaka wani dan tsagera a wata musayar wuta. A cewar sanarwar, a yayin da dakarun sintirin ke bugawa da wasu ‘yan tsageran ne sai wasu ‘yan tayar da kayar bayan su ka shiga kone konen gidajen jama’a da wuraren sana’o’insu saboda wai su ne ke tsegunta ma jami’an tsaro bayanai game da su. Nan da nan sai dakarun sintirin su ka koma wurin don su fatattaki ‘yan tsageran. Abin takaici, sai wani gwarzon soja ya kwanta dama sanadiyyar kare jama’a.

Sanarwar ta ce tun bayan abin bakin cikin nan da ya faru ranar 5 ga watan Afirilun wannan shekara, lokacin da wasu bata gari su ka kutsa cikin gidan yarin garin Owerri su ka kubutar da fursunoni 1,800 aka samu karuwar aikata manyan laifuka irin su sace sacen mutane, kwace motoci, fashi da makami, kashe kashe na ba gaira babu dalili da kuma kone kone a jihar Imo.

Sanarwar ta ce duk da gagarumar farfagandar da ‘yan tsageran IPOB/ESN, sauran bata gari da masu daure masu gindi ke yi don hana ‘yan Najeriya sanin gaskiyar al’amari game da kone konen Awo-Mmamma, rundunar sojin Najeriya za ta cigaba da aikinta yadda ya kamata.

Saurari rahoton Alphonsus Okoroigwe:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00


XS
SM
MD
LG