Rahoton da Farfasa Alubo da Dr Odetotinbo suka gabatar wurin bitar karawa juna ilimi ya nuna cikin jariri dubu daya da aka haifa a lokacin mulkin Murtala Nyako a jihar Adamawa dari hudu ke mutuwa.
Rashin ingantattun kayan aiki. magunguna da asibitoci suka jawo hakan. Masanan sun alakanta abun da ya faru a jihar da kasawar gwamnatin Nyako ta kebe wa fannin kiwon lafiya kashi goma sha biyar bisa dari na kason kudin jihar. Misali nera biliyan biyu da digo tara kacal aka kebewa fannin kiwon lafiya daga kasafin kudin 2014 a jihar dake da asibitoci 22 da likitoci 26 na nas 300 da sauran ma'aikatan kiwon lafiya 720.
Kungiyar da ake kira PAK da jami'ar Amurka dake Yola da kuma cibiyar kiwon lafiya a matakin farko na jihar Adamawa sun caccaki matakin da tsohon gwamnan ya dauka na kashe biliyan shida wajen gina wani katafaren asibitin Jamus.
Sun bayyana ana iya anfani da kudaden wajen gyara asibitoci 22 da samarda ingantattun kayan aiki.
Ga cikakken bayani.
Your browser doesn’t support HTML5