An Bukaci Buhari Ya Ziyarci Yankunan Da Boko Haram Ta Daidaita

Wani yanki da mayakan Boko Haram su ka daidaita a jihar Borno.

Yayin da kwamitin gwamnatin tarayya da aka kafa domin farfado da yankin arewa maso gabashin Najeriya ya isa jihar Adamawa, al’umar yankin sun ce babbar bukatarsu ita ce a maido da matakan tsaro

A cewar wasu mazauna yankin Madagali akwai bukatar jami’an tsaro da na kwastam da sauran hukumomi su koma yankin.

“Muna kira ga gwamanatin tarayya da a dawo da kananan ofisoshin ‘yan sanda da na kwastam da jami’an shige da fice da sauran ma’aikatan tarayya domin a samu mutanenmu su koma gida.” In ji Alhaji Muhammed Hassan, daya daga cikin matasan yankin.

Kwamitin ta da komadar yankin ya nuna damuwarsa mtauka kan yadda ya ga garin na Madagli, lura da yadda aka daidaita ababan more rayuwa da muhallan jama’a.

“Mun zagaya Madagali da Minchika, abubuwan da muka gani a Madagali kwarai ya tayar mana da hankali.” In ji Mista Adamu Kammale, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Madagali da Michika.

Ya kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya samu lokaci ya ziyarci yankin domin ya ganewa idonsa yadda al’amuran su ke.

Domin jin karin bayani dangane da wannan rahoto, saurari rahoton wakilin Sashen Muryar Amurka, Ibrahim Abdulaziz:

Your browser doesn’t support HTML5

An Bukaci Buhari Ya Ziyarci Yankunan Da Boko Haram Ta Daidaita- 3’13”