'yan Boko Haran na anfani da hare-haren ne domin su nuna suna nan har yanzu da karfinsu.
Saidai ta bakin gwamnan "a zahiri jami'an tsaron Najeriya sun riga sun ci karfin 'yan Boko Haram". Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda ya ziyarci wadanda suka jikata dake samun jinya a asibitin koyaswa na Jami'ar Maiduguri.
Inji gwamnan irin wadannan hare-haren ba zasu tsoratar da su ba, kuma za'a cigaba da farauto 'yan ta'adan ko ta halin kaka domin wanzar da zaman lafiya mai dorewa a jihar..
'Yan Boko Haram sun yi anfani da 'yan mata biyu ne wurin tayar da bam din. Sun 'yan matan sun tarwatsar da kansu inda nan take suka raunata mutane 18 kana mutum daya ya rasa ransa.
Inji gwamnan Shettima da yaddar Allah an riga an ci karfin 'yan Boko Haram. Yace za'a kawo karshensu. Yace yanzu basu isa su rike koina ba saboda an fatattakesu daga garuruwan da suka cafke.
Gwamnatin Borno zata dauki duk matakan da suka dace na ganin ba'a tozarta mutanen jihar ba kuma za'a yi bikin Maulidi lafiya da bikin Kirsimati lafiya ba tare da tsangwama ba.
Yawancin wadanda suka jika 'yan makaranta ne dake kan hanyarsu ta zuwa makarantunsu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.