An Bukaci Dakatar da Taron Kasa

Wasu daga cikin wakilan taron kasa.

A zauren taron kasa wasu wakilai sun bukaci a dakatar da taron sai an kawo karshen kashe-kashe da sace-sacen mutane dake son zama ruwan dare gama gari a kasar Najeriya.
Biyo bayan hare-haren bamabamai da aka kai akan Nyanya kusa da cikin birnin Abuja ranar Litinin, wakilan taron sun bukaci a dakatar da taron sai gwamnati ta kawo karshen kashe-kashe da sace-sace a kasar.

Tsohon mataimakin sifeton 'yan sanda Abdulmunmuni Abubakar shi ya kawo kudurin a dakatar da taron kasa har sai an shawo kan kashe-kashe da sace mutane a sassan Najeriya daban daban. Hakan na zuwa ne lokacin da taron ya cika da juyayi akan harin bam na Nyanya da ya rutsa da rayuka fiye da saba'in da raunata wasu fiye da dari da hamsin.

To sai dai wasu a taron na ganin domin kashe-kashen sun tinkaro kokuwar birnin tarayya ne. Dr Hannatu Ibrahim wakiliya a taron tace dukansu su gayawa juna gaskiya. Idan ta kama a je a samu shugaban kasa a je a fada masa gaskiya baro-baro ba tare da jin wani shakka ba. A je a fada masa lamarin ya isa haka. Rayuka na salwanta. Ya dakatar.

Amma Ambassador Ladan Shuni yace sam babu sakaci a bangaren gwamnati ko kuma hannun gwamnati cikin abubuwan dake faruwa kamar yadda wasu wakilan taron ke gani Boko Haram ta kasu kashi-kashi. Ladan Shuni yace babu yadda za'a ce shugaban kasa da yake son mulkin jama'a a ce yana da hannu a kisan mutane. Idan ya kashe mutane wa zai mulka? Mutanen dake irin wadannan zarge-zargen su fito da shaida kwakwara su tabbatar da abubuwan da suke cewa. Yace a tuna da can an yi fadi cewa Najeriya zata wargaje. Yace masu fadan haka zasu ji kunya.

Ladan Shuni yace makiyan Najeriya suke fada cewa Najeriya zata wargaje a shekarar 2015. Amurka ta fada, wato Amurka tana cikin makiyan Najeriya. Gadhafi ma makiyin Najeriya ne amma ya tafi. Yace a duk duniya babu kasa da take da banbance bandance irin Najeriya amma ana tare dunkule a matsayin kasa daya.

To sai dai Buba Galadima daga Yobe yana ganin lamarin daban da Ladan Shuni. Yace a Najeriya yanzu babu wani abu da zai auku a kawar da siyasa ciki. Dalili ke nan da PDP tace APC ce ta dasa bam da ya kashe mutane a Nyanya. Su da suka san sun dasa bam ai sun je Kano suna ta nishadi suna raye-raye suna shaye-shaye. Basu damu da rayukan da kasar tayi asara ba a Nyanya. Idan da wata kasa ce hakan ya faru tare da sace yara mata a jihar Borno to ko shugaban yana muhawara a majalisar dinkin duniya zai bari ya dawo kasarsa. Shugaban ya nuna rashin imani akan abubuwan dake aukuwa.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bukaci a Dakatar da Taron Kasa har Sai An Kawo Karshen Kashe-kashe - 3'01"