An Baiwa Babban Akanta Janar Na Jihar Bauchi Wa’adi Ya Biya Albashi

Bauchi

Majalisar Dokokin jihar Bauchi ta baiwa babban akanta janar na jihar wa’adin mako guda daya biya dukkan ma’aikatan jihar da aka kammala aikin tantancesu albashi.

Wannan hukunci da majalisar ta dauka ya biyo bayan gayyata ta musamman ne da aka yiwa akanta janar din da kwamishinan kudi da kwamishinan kananan hukumomi, dakuma shugaban kwamitin tantance ma’aikatan jihar da aka shafe kwanaki biyu suna amsa tambayoyi daga yan majalisar dan gane da rashin kasa biyan ma’aikatan jihar bauchin da kuma yan Fansho na tsawon watanni biyu zuwa uku.

A wata ganawa da manema labarai dan Majalisar Dokoki mai wakiltar mazabar Kirfi, Ibrahim Galadima Badara, ya tabbatar da cewa Akanta janar din ya gaya musu cewa zai biya ma’aikatan.

Shima da yake wa taron yan jarida bayani shugaban kwamitin tantance ma’aikatan, Barista Abubakar Abdulhamid, yayi bayani game da aikin tantancewar. Inda yace yanzu haka sun tantance mutane wajen Dubu 32, wanda suka hada da ma’aikata na jiha dana kananan hukumom da masu karbar Fansho na jiha dana Kananan hukumomi.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Baiwa Babban Akanta Janar Na Jihar Bauchi Wa’adi Ya Biya Albashi - 2'36"