An Ba 'Yan Jarida Wani Horo Akan Kiyaye Cutar Kolera A Niger

Hukumar kiwon lafiya ta duniya na ba ‘yan jarida na jihar Tahoua horo gameda annobar cutar kolera da jihar ke fama da ita.

Hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da kiwon lafiya da ake kira OMS a takaice ta takaddamar da wani shiri na ba ‘yan jarida horo, wato 'yan jaridar gidajen rediyon gwamnati da masu zaman kansu, da na karkara a jihar Tahoua, musamman wadanda suka fito daga gundumomin da suka yi fama da cutar kolera ko wadanda har yanzu akwai annobar a cikin su, ciki harda Keita, da Madaoua, da Malbaza da Birnin N'Konni duk akan kiyaye cutar kolera.

Dr. Amadu Adamu, shine shugaban hukumar asibiti na jihar Tahoua da ya wakilci gwamnan jihar a wurin bude taron. A hirar da sashen hausa yayi da shi, ya bayyana makasudin baiwa ‘yan jarida wannan horon a karkashin innuwar hukumar ta OMS, inda ya ce an yi taron ne don karfafa duk wadanda zasu taimaka wajen bada bayanai musamman gidajen radiyo gameda yaki da cutar kolera.

Daga cikin mutane 294 da suka kamu da cutar kolera a gundumomin Keita, Madaoua, Malbaza da Birnin N'Konni a cikin jihar ta Tahoua, mutane 12 ne yanzu suka riga mu gidan gaskiya.

Shatima Ali Bagale, shine wakilin hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da kiwon lafiya a Jihar Tahoua, yayi karin bayyani gameda abinda suke jira ga ‘yan jaridar da suke tallafawa domin a basu horon akan annobar ta kolera. Ya ce suna sa ran idan ‘yan jaridar sun koma cikin al’umma zasu wayarwa jama’a da kai akan yadda zasu kiyaye kamuwa da cutar.

A nasu bangaren, ‘yan jaridar da ke halartar wannan taron da hukumar OMS keyi, sun bayyana abubuwan da suka karu da su, sun kuma ce sun gamsu da bayannan da aka yi masu kuma an nuna musa yadda zasu taimakawa sauran jama’a don cetarsu daga wannan cutar.

Ga labari cikin sauti daga Harouna Mamane Bako.

Your browser doesn’t support HTML5

An Ba 'Yan Jarida Wani Horo Akan Kiyaye Cutar Kolera A Niger - 3'48"