Nahiyar Afrika na kan gaban yankunan da hukumar lafiya ta duniya OMS ta ayyana a matsayin mafi fama da masassarar cizon sauro, dalili kenan da shugabannin kungiyar tarayyarAfrika a yayin taron da suka gudanar a baya bayan nan a Nouakchot suka yanke shawarar sake jan damara, mafarin wannan kamfe din kenan da aka yiwa lakabi da Zero Palu Je M’engage.
Dr. Iliyasu Idi Mainasara, shine ministan kiwon lafiya na Nijer ya duk shekara ana samun hasarar miliyoyin rayuka, akan haka ne shugabannin Afrika suka dauki wannan matakin don ganin cewa an magance wannan matsalar nan da shekarar 2030.
Kyakkyawar niyar da gwamnatin Nijer ta nuna a ‘yan shekarun nan game da yaki da zazzabin cizon sauro ya sa gwamnatin Amirka saka wannan kasa a cikin jerin wadanda ke samun tallafi a wannan fanni.
Koda yake jama’a na murna a dangane da manufofin wannan kamfen da ake ganin zai kawo sauyi a rayuwar talakawa, masu fafitika irinsu Hajiya Amina Garba na kiraye kirayen a yi adalici wajen tafiyar da wannan shiri.
Uwargidan shugaban kasar Nijer Hajiya Aishatu Issouhou, dake jagorancin gidauniyar Guri Vie Meilleure ce aka dorawa nauyin tafiyar da wannan kamfe din na Zero Palu Je M’engage yayinda kasar Amirka, a ta bakin jakadanta a Nijer Eric P. Whitaker, ta kara jaddada aniyar cigaba da tallafawa wannan kasa don ganin an ci nasarar yaki da zazzabin cizon sauro.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum