An ba kungiyoyin kwallon kafar nahiyar turai damar jinkirta sakin ‘yan wasansu da za su kara a gasar cin kofin nahiyar Afirka har zuwa makon da za a fara gasar.
Ka’idojin FIFA sun nuna cewa, wajibi ne a saki ‘yan wasan su koma kasashensu na asali a Afirka nan da wannan ranar Litinin da aka shata.
Amma yanzu kungiyoyi za su iya rike ‘yan wasan har sai ranar 3 ga watan Janairu kafin su sake su.
Za dai a fara gasar cin kofin nahiyar ta Afirka da kasashe 24 a ranar 9 ga watan Janairu a birnin Yaounde da ke Kamaru.
Za kuma a kammala gasar da wasan karshe a ranar 6 ga watan Fabrairu.
Mataimakin Sakatare Janar na kungiyar kwallon kafa ta FIFA Mattias Grafstrom ne ya rubutawa hukumar wasika a ranar Asabar da hukumomin gasa da ake bugawa a turai dauke da wannan sauyi da aka yi, wasikar da kamfanin dillancin labarai ta AP ta ce ta gani.