“Hukumar kwallon kafa ta CAF, ta sahale Alex Iwobi ya buga wasansu da Lesotho” Shafin Super Eagle na Twitter ya wallafa ranar Talata.
An gano cewa Iwobi yana dauke da cutar ne, a lokacin da aka yi wa ‘yan wasan Najeriya gwajin cutar gabanin wasansu da Jamhuriyar Benin a ranar Asabar.
“Amma gwaje-gwajen baya-bayan nan da aka yi masa, sun nuna cewa ya rabu da cutar. Dakin binciken cututtuka na Clina Lancet da ke Legas ne ya gudanar da gwajin. Hakan na nufin, Iwobi zai buga wasan na yau.” In ji hukumar ta Super Eagles.
Wani hoton bidiyo da shafin na Super Eagles ya wallafa, ya nuna dan wasan na Everton, yana mika godiyarsa.
“Ya zama dole na bi ka’idojin da hukumar kwallon kafa ta FIFA da CAF suka gindiya, inda na kebe kaina a daki.”
“Ina godiya ga dukkan wadanda suka nuna min kauna, musamman shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, da abokan wasana.”
Tsohon dan wasan na Arsenal, ya ce bai ji alamun cutar sosai ba, abin da ya sa bai galabaita ba.
Najeriya, wacce ta riga ta samu gurbi, na shirin karawa da kasar Lesotho a yau, a ci gaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON da za a yi a Kamaru.