Barkewar cutar da ta shafi darurruwar mutane da dama, na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Kamaru ke shirin karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afrika, ko AFCON, da za a fara ranar 9 ga watan Janairu.
Yaounde, wacce za ta karbi bakuncin tawagogin kasashen Afirka takwas a gasar kwallon kafa ta nahiyar, ta ba da rahoton bullar cutar kwalara a kalla 100.
Ministan kiwon lafiya na Kamaru Manaouda Malachie a cikin wata sanarwa da aka fitar a wannan makon ya ce dubban fararen hula a babban birnin Yaounde da Ekondo-Titi, wani gari masu harsehen Ingilishi a yammacin kasar, na fuskantar barazanar kamuwa da cutar kwalara.
A wani taron manema labarai, magajin garin Yaounde Luc Messi Atangana ya ce yana tsaftace birnin tare da inganta samar da ruwan sha don dakatar da yaduwar cutar kwalaran.
Messi ya ce barkewar cutar ta samo asali ne sakamakon karuwar sharar da fararen hula ke zubarwa a kan tituna, kuma ya dauki hayar manyan motoci 30 don karawa wasu 200 da ke share garin Yaounde daga gurbataccen shara. Yana sa ran Yaounde zai kasance mai tsabta kuma ya kubuta daga cutar kwalara cikin makonni biyu masu zuwa.
Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce an garzaya da marasa lafiya dari da dama zuwa asibitoci a Yaounde da Ekondo-Titi. Gwamnati ta ce ta samu rahoton mutuwar mutane akalla 13 masu nasaba da kwalara a garuruwan biyu tun ranar Litinin.
Ma'aikatar lafiyar ta kuma kara da cewa barkewar cutar kwalara na iya yin wuya a shawo kanta. Kasa da kashi 30 cikin 100 na al'ummar kasar na ziyartar asibitoci ko dai saboda jahilci ko kuma saboda wasu fararen hula sun fi son magungunan gargajiya na Afirka. Ma’aikatan lafiya na kira ga fararen hula da su mika wadanda ake zargi da kamuwa da cutar kwalara zuwa asibitoci mafi kusa.